Mark 10

Kashen Aure

1Sai Yesu ya tashi daga nan ya tafi yankin Yahudiya, da kuma ƙetaren Urdun. Taron mutane suka sāke zuwa wurinsa, ya kuma koya musu kamar yadda ya saba.

2Waɗansu Farisiyawa suka zo suka gwada shi, ta wurin yin masa tambaya, cewa, “Daidai ne bisa ga doka, mutum yǎ saki matarsa?”

3Ya amma ya ce, “Me Musa ya umarce ku?”

4Suka ce, “Musa ya ba da izini mutum yǎ rubuta takardar saki, yǎ kuma kore ta.”

5Yesu ya ce, “Saboda taurin kanku ne, Musa ya rubuta muku wannan doka. 6Amma a farkon halitta, Allah ya ‘halicce su miji da mace.’
Far 1.27
7‘Saboda wannan dalili, mutum zai bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yǎ manne wa matarsa, 8su biyun kuma za su zama jiki ɗaya.’
Far 2.24
Saboda haka, su ba mutum biyu ba ne, amma mutum ɗaya.
9Domin haka, abin da Allah ya haɗa, kada mutum yǎ raba.”

10Da suna cikin gida kuma, sai almajiran suka tambayi Yesu game da wannan. 11Ya amma ya ce, “Duk wanda ya saki matarsa, ya auri wata, yana da laifin aikata zina a kan matar da ya saki. 12In kuma ta saki mijinta ta auri wani, zina take yi.”

Yesu da Ƙananan Yara

13Mutane suka kawo ƙananan yara wurin Yesu don yǎ taɓa su, amma almajiran suka kwaɓe su. 14Da Yesu ya ga haka, sai ya yi fushi, ya ce musu, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su, gama mulkin Allah na irin waɗannan ne. 15Gaskiya nake gaya muku, duk wanda bai karɓi mulkin Allah kamar ƙaramin yaro ba, ba zai taɓa shiga mulkin ba.” 16Sai ya ɗauki yaran a hannuwansa, ya ɗibiya musu hannuwansa, ya kuma albarkace su.

Saurayi Mai Arziki

17Da Yesu ya kama hanya, sai wani mutum ya ruga da gudu ya zo wajensa, ya durƙusa a gabansa, ya ce, “Malam nagari, me zan yi domin in gāji rai madawwami?”

18Yesu ya amsa, ya ce, “Don me kake ce da ni mai nagarta? Ai, ba wani nagari sai Allah kaɗai. 19Ka dai san dokokin: ‘Kada ka yi kisankai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka ba da shaida ta ƙarya, kada ka cuci wani, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’
Fit 20.12; M Sh 5.16-20


20Mutumin ya ce, “Malam, ai, tun ina yaro na kiyaye duk waɗannan.”

21Yesu ya kalle shi da ƙauna, ya ce, “Abu ɗaya ka rasa, ka tafi ka sayar da duk abin da kake da shi, ka ba wa matalauta, za ka kuwa sami dukiya a sama. Saʼan nan ka zo ka bi ni.”

22Da jin wannan, sai mutumin ya ɓata fuskarsa, ya tafi da baƙin ciki, domin yana da arziki sosai.

23Yesu ya dudduba, sai ya ce wa almajiransa, “Yana da wuya fa masu arziki su shiga mulkin Allah!”

24Almajiransa suka yi mamakin kalmominsa. Amma Yesu ya sāke ce musu, “ʼYaʼyana, yana da wuya fa a shiga mulkin Allah! 25Ya fi sauƙi raƙumi yǎ shiga ta kafar allura, da mai arziki yǎ shiga mulkin Allah.”

26Almajiran suka yi mamaki ƙwarai, suka ce wa juna, “To, wa zai sami ceto ke nan?”

27Yesu ya kalle su, ya ce, “Ga mutum kam, wannan ba mai yiwuwa ba ne, amma ga Allah wannan mai yiwuwa ne; dukan abubuwa masu yiwuwa ne ga Allah.”

28Bitrus ya ce, “Mun bar kome domin mu bi ka!”

29Yesu ya amsa, ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, babu wanda zai bar gida, ko ʼyanʼuwa maza da mata, ko mahaifiya, ko mahaifi, ko ʼyaʼya, ko gonaki saboda ni, da kuma bishara, 30saʼan nan yǎ kāsa samun ninkinsu ɗari a zamanin yanzu, (na gidaje, da ʼyanʼuwa mata, da ʼyanʼuwa maza, da uwaye, da ʼyaʼya, da gonaki— amma tare da tsanani), a lahira kuma yǎ sami rai madawwami. 31Amma da yawa da suke na farko, za su zama na ƙarshe, na ƙarshen kuma za su zama na farko.”

Yesu Ya Sāke Yin Zancen Mutuwarsa

32Suna haurawa a hanyarsu zuwa Urushalima ke nan, Yesu yana a gaba, almajiran suna binsa suna mamaki, waɗanda suke bi kuma suna ji tsoro. Ya sāke kai Sha Biyun nan gefe, ya gaya musu abin da zai faru da shi. 33Ya ce, “Za mu haura zuwa Urushalima, za a bashe Ɗan Mutum, ga manyan firistoci da malaman dokoki. Za su yi masa hukuncin kisa, a kuma ba da shi ga Alʼummai, 34waɗanda za su yi masa baʼa, su tofa masa miyau, su yi masa bulala, su kuma kashe shi. Bayan kwana uku kuma yǎ tashi.”

Roƙon Yaƙub da Yohanna

35Sai Yaƙub da Yohanna, ʼyaʼyan Zebedi maza suka zo wurinsa suka ce, “Malam, muna so ka yi mana duk abin da muka roƙa.”

36Ya tambaye su, ya ce, “Me kuke so in yi muku?”

37Suka amsa suka ce, “Ka bar ɗayanmu yǎ zauna a damarka, ɗayan kuma a hagunka, a cikin ɗaukakarka.”

38Yesu ya ce, “Ba ku san abin da kuke roƙo ba. Za ku iya shan kwaf da zan sha, ko a yi muku baftisma da baftismar da aka yi mini?”

39Suka ce, “Za mu iya.”

Yesu ya ce musu, “Za ku sha kwaf da zan sha, kuma yi muku baftisma da aka yi mini,
40amma zama a damana ko haguna, ba ni nake ba da izinin ba. Waɗannan wurare na waɗanda aka riga aka shirya musu ne.”

41Da sauran goman suka ji wannan, sai suka yi fushi da Yaƙub da Yohanna. 42Yesu ya kira su ya ce musu, “Kun sani waɗanda aka san su da mulkin alʼummai sukan nuna musu iko, hakimansu ma sukan gasa musu iko. 43Ba haka ya kamata yǎ zama da ku ba. A maimakon, duk wanda yake so yǎ zama babba a cikinku, dole yǎ zama bawanku. 44Duk wanda kuma yake so yǎ zama na farko, dole yǎ zama bawan kowa. 45Gama ko Ɗan Mutum ma, bai zo domin a bauta masa ba, amma don yǎ yi bauta, yǎ kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.”

Bartimawus Makaho Ya Sami Gani

46Sai suka iso Yeriko. Saʼad da Yesu da almajiransa tare da taro mai yawa suke barin birnin, wani makaho da ake kira Bartimawus kuwa, (wato, Ɗan Timawus), yana zaune a gefen hanya yana bara. 47Da ya ji cewa Yesu Banazare ne, sai ya ɗaga murya, yana cewa, “Yesu Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!”

48Mutane da yawa suka kwaɓe shi, suka ce yǎ yi shiru, amma ya ƙara ɗaga murya yana, cewa, “Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!”

49Yesu ya tsaya, ya ce, “Ku kira shi.” Sai suka kira makahon suka ce, “Ka yi farin ciki! Tashi tsaye! Yana kiranka.” 50Ya jefar da mayafinsa waje ɗaya, ya yi wuf, ya zo wurin Yesu.

51Yesu ya tambaye shi, ya ce, “Me kake so in yi maka?” Makahon ya ce, “Rabbi, ina so in sami ganin gari.”

52Yesu ya ce, “Je ka, bangaskiyarka ta warkar da kai.” Nan da nan, ya sami ganin gari, ya kuma bi Yesu suka tafi.

Copyright information for HauSRK